ABNA24 : A yayin saukar firayi ministan na Koriya ta Kudu a filin saukar jiragen sama a Tehran, ya sami tarbar ministan tituna da gina birane, Muhammad Islami.
Daga cikin wadanda zai gana da su da akwai Shugaban kasar Dr. Hassan Rauhani, mataimakin shugaban kasar Ishak Jihangiri, sai kuma kakakin majalisa Muhammad Bakir Qalibaf. Har ila yau zai yi wata ganawar da Ali Larijani, mai bai wa jagoran juyin musulunci shawarar.
A yayin ziyarar tasa, Pira ministan na kasar Korea ta kudu,z ai ziyarci kamfanonin kasarsa a Iran da su ka hada “ Samsung da LG”.
342/